Kayi Duk Abinda Zaka Iya Don Ganin PDP Ta Lashe Kano, Kaduna, Jigawa, Niger – Wike Ga Maƙarfi

Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bukaci tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ahmed Makarfi da ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta yi nasara a jihohin Arewa.

Wike yace ya kamata Makarfi ya tabbatar da cewa PDP tayi nasara a jihohin Kano, Jigawa, Niger, da Kaduna.

Wike Ya yi wannan jawabi ne a wajen kaddamar da yankin Sandfilled Ogbunabali a Fatakwal, babban birnin jihar a ranar Talata.

A nasa bangaren tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi ya bukaci yin duk mai yiwuwa wajen ganin wasu ‘yan takarar shugaban kasa sun koma jam’iyyar PDP.

Ya kuma bukaci jam’iyyar Labour Party, da dan takararta na shugaban kasa Peter Obi da takwaransa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso da su koma PDP.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna yace Obi da Kwankwaso su hadiye burinsu su koma PDP, don tabbatar da Nasarar Jam’iyyar da Dan takararta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *