Kotu Ta Hana EFCC Karɓe Kaddarorin Gwamna Matawalle Na Zamfara
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar na neman kwace wasu kadarori guda shida a Abuja da ke da alaka da Gwamna Bello Matawale na Jihar Zamfara.
Mai shari’a Inyang Ekwo a jiya ya bayyana cewa ba za a iya gabatar da bukatar a kan gwamnan ba saboda tanadin sashe na 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.
Kotun ta ci gaba da cewa hukumar EFCC ba ta da hurumin fara duk wani tuhuma da ake yi wa gwamnan a lokacin da yake kan karagar mulki.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta lissafa kadarorin a matsayin filaye 1327, Zone A05, 2934, 730, da fili 2804B, dukkansu dake a Zone A06, Cadastral Zone, gundumar Maitama; da 729, Idu Industrial Layout and Plot 575 BOO a gundumar Kubwa a matsayin wadanda take so ta kwace daga hannun Gwamnan.
EFCC ta ci gaba da zargin cewa gwamnan ya kwashi kusan Naira biliyan 2.1 daga ma’aikatar kudi ta jihar zuwa hukumar kula da zuba jari da kasuwanci da ke karkashin ofishinsa kuma ya yi amfani da wasu kamfanoni da ofishin canji (BDC) wajen karkatar da kudaden
