Babbar Kotun masana’antu ta kasa ta sanya ranar Laraba 21 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan bukatar da gwamnatin tarayya.
Gwamnatin ta shigar da kara a gabanta kan kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) kan dogon lokacin da ta dauka tana yajin aiki.
Mai shari’a Peter Hamman ya tsayar da ranar Litinin ne bayan da babban lauyan gwamnatin tarayya, Mista James Igwe, ya shigar da kara a gaban kotun.
Lauyan ya nemi kotu ta ba da umarnin hana ASUU ci gaba da yajin aikin da ke ci gaba da yi a fadin kasar.
