Lalacewar Asibitin Sir Sanusi Laifin Gwamnatin Ganduje Ne – Abba Gida-Gida

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya ta’allaka laifin lalacewar Asibitin Sir Sanusi daya daga cikin tsofaffi kuma manyan cibiyoyin kiwon lafiya a jihar da rashin kula na gwamnatin baya ta Ganduje.

Gwamnan ya ce a yayin ziyarar da ya kai a Asibitin jim kadan bayan dawowarshi daga wata tafiya da ya yi, ya ce abinda ya gane wa idanunsa bai ji dadi ba halin da ya ga Asibitin na ciki.

Hakazalika, Abba ya ce dukda lalacewar Asibitin ya samu wata jajirtacciyar ma’aikaciyar wucin gadi da ta ke ta faman taimakon jama’a kuma nan take ya bada umurnin a dauke ta aiki na dindindin.

Yanzu haka dai gwamnan ya ce ya bayar da umurnin a fara gyaran Asibitin domin samun walwala da inganta yanayin marasa lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *