Majalisa Dattawa Ta Sanar Da Ranar Da Za Ta Amince Da Kasafin Kuɗin Baɗi
Majalisar dokokin kasar nan za ta amince da kasafin kudin shekarar 2023 a ranar Alhamis.
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya tabbatar da hakan a zaman majalisar a ranar Laraba.
Ya ce za a daidaita kasafin da majalisar wakilai kafin ranar Alhamis.
A cewar sa, an bayyana haka ne domin tabbatar da cewa an kiyaye da’irar aikin kasafin kudin watan Janairu zuwa Disamba.
A ranar 7 ga watan Oktoba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin kasafin kudin 2023 na Naira tiriliyan 20.5 ga majalisar dokokin kasar.
Lawan ya ce bayan zartar da kasafin kudin, majalisar dokokin kasar za ta dage ayyukan majalisar domin hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Shi ma kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a jiya ya tabbatar da cewa za a zartar da kasafin a gobe.
Ya yi wannan jawabi ne ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
