Kwamitin majalisar dattawa mai kula da satar mai na Adhoc, ya ce ya fara bincike kan al’amuran da suka shafi satar mai da ayyukan da ba bisa ka’ida ba a yankin Neja Delta.
Shugaban kwamitin, Bassey Akpan ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a lokacin da suka isa filin jirgin sama na Fatakwal cikin mako.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Akpan ya koka da yawaitar satar danyen man fetur da ake yi a Najeriya, yana mai cewa abin damuwa ne.
Ya ce kasar ta yi hasarar makudan kudaden da aka samu tare da kasa cika kason da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta ware.
