Mataimakin Shugaban APC Lukman Yace Tarwatsa Tsarin Ilmi Ne A Biya ASUU Albashi Suna Yajin Aiki
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Salihu Lukman ya ce har sai gwamnatin tarayya ta bullo da tsarin rashin aiki, babu albashi, mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) za su ci gaba da rike kasar nan, don yin fansa saboda yajin aikin da suke yi.
Lukman ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja yayin wata tattaunawa da Manema Labarai da wasu zababbun ‘yan jarida, inda ya jaddada cewa, al’ada ce mai barna a biya ma’aikatan dake yajin aiki albashi.
Ya na mai ra’ayin cewa zuba jari a fannin ilimin jama’a abu ne da bai kamata a yi wasa da shi ba.
Jigon jam’iyyar ya lura cewa ya kamata Najeriya ta koma kan tsohon tsarin da manufofin IMF/Bankin Duniya suka ruguza, yana mai jaddada cewa babu wata kasa da za ta ci gaba ta hanyar samar da kudade masu zaman kansu na bangaren ilimi.
