Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 1,175 kan kowace lita zuwa naira 1,075, wanda ke nuna ragin naira 100.
A cikin wata sanarwa da matatar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan saukar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, tare da cewa an dauki matakin ne bisa sabon tsarin farashin da kamfanin ya fitar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa matatar ta rage farashin man dizal zuwa naira 1,430 kan kowace lita daga tsohon farashin naira 1,620.
Matatar ta jaddada kudurinta na taimakawa wajen karfafa tsaron makamashi a Najeriya, tare da la’akari da halin tattalin arzikin da al’ummar kasar ke ciki, kamar yadda wani babban jami’in kamfanin ya bayyana.
Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne karo na farko da aka rage farashin man bayan karin sau uku a jere da aka yi a makonnin baya, wanda ya haddasa tashin farashin man sosai a kasuwa.
