Jagoran Jam’iyyar NNPP, Sen Rabiu Musa Kwankwaso a ya karɓi ziyarar girmamawa daga wata ƙungiyar matasa tare da wakilci daga gidan Tsohon Dan takarar Gwamnan Jihar Kano Dr. Yusuf Gawuna, wadda aka fi sanin Kingiyar da ‘Bulo Takwas Muke su a zare, a debe mu a kawo mu gidan Jagora.’
Ziyarar ta samu jagoranci daga Hon. MB Aliyu, Dan Majalisar Jiha na karamar Hukumar Nassarawa, inda suka kawo gaisuwar barka da Sallah da fatan alkhairi ga Jagora, tare da nuna cikakken goyon baya ga tafiyar siyasa da ci gaban al’umma.
Me za ku ce?
