Mutane 10 sun mutu a hatsarin mota a jihar Niger – FRSC

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutane 10 sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Niger.

Hukumar ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin da misalin ƙarfe 8:20 na safe a yankin Tafa, a kan hanyar Tafa zuwa Gujeni (Malam Tanko), inda wata motar tanka kirar DAF mai lamba FKY136XD ta yi hatsari.

A cewar FRSC, hatsarin ya rutsa da mutane 33, dukkansu maza ne. Daga cikinsu, mutane 10 sun rasa rayukansu, yayin da 20 suka jikkata, sai kuma mutum uku da suka tsira ba tare da wani rauni ba.

Hukumar ta danganta faruwar hatsarin da gudun wuce gona da iri, wanda ya sa direban motar ya rasa ikon sarrafa ta. Haka kuma, an bayyana cewa motar na ɗauke da kaya da kuma fasinjoji a lokaci guda, abin da ya sa hatsarin ya fi muni.

Jami’an FRSC sun isa wurin da hatsarin ya faru cikin gaggawa, inda suka ceto mutane 23 da rai, tare da kai waɗanda suka samu raunuka zuwa Asibitin Umar Musa General Hospital da ke Sabon Wuse domin samun kulawa.

An kuma kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa ɗakin ajiye gawa na asibitin.

Shugaban hukumar FRSC ya ce hatsarin na daga cikin waɗanda za a iya kauce musu, inda ya shawarci direbobi da su rika bin dokokin hanya, su rage gudu, tare da guje wa ɗaukar fasinjoji a motocin da ba su dace da hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *