Mutane hudu sun mutu a turmutsitsin rabon tallafin Ramadan a Katsina

A kalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin da ya auku yayin rabon tallafin Ramadan a unguwar Kofar-Guga da ke birnin Katsina, lamarin da ya jefa al’umma cikin jimami a wannan wata mai alfarma.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Aliyu Abubakar, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na dare ranar 26 ga Fabrairu, 2026, bayan samun kiran gaggawa kan taruwar jama’a masu yawa a gidan wani attajiri mai taimakon al’umma domin karbar tallafin shekara-shekara, wanda ya rikide zuwa turmutsitsi.

Ya ce an tura jami’an ‘yan sanda cikin gaggawa zuwa wurin tare da garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa domin samun kulawar likitoci, sai dai cikin takaici, mutane hudu daga cikin su sun rasu, yayin da Kwamishinan ‘Yan Sanda, Mista Bello Shehu, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da umarnin gudanar da bincike da kuma kira ga masu raba tallafi su rika sanar da hukuma domin samar da isasshen tsaro a nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *