Hukumar NACA ta bayyana cewa Najeriya na shirin karɓar maganin rigakafi mai ƙarfi da sauƙin amfani, wanda zai iya canza tarihin yaduwar HIV a ƙasar. A cikin wata sanarwa da Shugabar Hulɗa da Jama’a ta NACA, Toyin Aderibigbe, ta fitar ranar Litinin, an bayyana cewa an samu amincewar hukumar NAFDAC domin shigo da maganin Lenacapavir cikin ƙasa.
Lenacapavir magani ne da ake yi ta allura sau biyu kacal a shekara, wanda ke sa shi ya fi sauƙi a amfani fiye da sauran magungunan rigakafin HIV da ake sha kullum. Gwaje-gwajen kimiyya sun nuna cewa maganin yana bayar da kashi 100 cikin 100 na kariya daga kamuwa da cutar HIV a binciken asibiti.
Hukumar ta ce gwamnatin Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen fara amfani da maganin a matsayin rigakafin kafin kamuwa da cuta (PrEP), a wani ɓangare na ƙudurin ƙasa na yaƙi da HIV da rage yaduwar cutar. Ana sa ran Lenacapavir zai samu sauƙin farashi na dala 40 kawai a shekara ga kowane mutum, sakamakon yarjejeniyar bayar da lasisi ga kamfanonin ƙera magungunan generic, tare da niyyar shigar da shi Najeriya da wasu ƙasashe 119 masu ƙarami da matsakaicin ƙarfin tattalin arziki.
