NECO Tana Cigaba Da Riƙe Sakamakon 2021 Na Jarabawar Ɗaliban Zamfara, Zata Saki na Shekarar 2022
Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Gwamnati jihar Zamfara ta bayyana cewa an kammala biyan kudin jarabawar NECO inda ta bayyana cewa zata saki sakamakon jarabawar a karshen wannan watan.
Wannan na kunshe ne acikin wata sanarwar da ministan yada labarun jihar Hon. Ibrahim Magaji Dosara ya rabawa manema labarai a Gusau babban birnin jihar.
Kwamishinan ya shawarci iyayen yaran da suka zauna jarabawar NECO 2022, dasu ziyaraci makarantu a karshen watan Satumban 2022 domin ganin sakamakon.
Ya bayyana cewa daliban da suka zauna jarabawar zasu iya ganin sakamakon nasu ta yanar zigo domin samun gurbin shiga manyan makarantu daban-daban, kafin tura sakamakon ga Hukumar kula da Jarabawa ta Jihar Zamfara.
Dosara ya kuma bukaci iyaye dasu kara hakuri suna cigaba da tattaunawa akan fitar da sakamakon jarabawar ta NECO ta Shekarar 2021.
“Gwamnatin jihar ba zatayi kasa a giwa ba wurin ganin tabbatar da bangaren Ilimi ya cigaba ta ko wane bangare,”.
