NPC Ta Gudanar Da Ƙidayar Gwaji A Ƙananan Hukumomin Dake Fama Da Matsalar Tsaro A Sokoto.

NPC Ta Gudanar Da Ƙidayar Gwaji A Ƙananan Hukumomin Dake Fama Da Matsalar Tsaro A Sokoto.

Daga Wakiliyar Mu Amira Salisu Batsari.

Hukumar Ƙidayar ta kasa ta gudanar da Ƙidayar Jama’a ta gwaji a ƙananan Hukumomi 9 na Jahar Sokoto.

Kananan hukumomin sun haɗa da, Wurno, Rabah, Tureta, waɗanda suke fama da harin yan bindiga.

Sauran sun hada da, Shagari, Wamakko, Gwadabawa, Silame, Sokoto ta Kudu, da kuma Tambuwal.

Da yake jawabi bayan ya duba yanda Ƙidayar ke gudana a yankunan, kwamishinan Ƙidayar mai kula da jahar Sokoto Chiso Dattijo, ya nuna gamsuwar sa na yadda mazauna yankin suka bada haɗin kai ga ma’aikatan dake shata ƙidayar.

” Naji dadi yadda kidayar ke tafiya, musamman a yankunan da suke fuskantar harin yan bindiga.”

” Dole na yabawa ma’aikata, da masu rike sarautun Gargajiya, da hukumomi, da mazauna yankin ta yadda suka bada hadin Kai,” ya fada.

Kwamishinan ya bayyana cewa kidayar na tafiya yadda ya kamata, Babu rahoton da ya nuna cewa ma’aikatan nasu sun fuskanci wata matsala.

Wani daga cikin mazauna yankin, Yusuf Aliyu Gidan Inda, Wanda yayi bayani akan amfanin kidayar ga Cigaban kasa, ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.

” Muna bukata ga Gwamnati da tayi duk Mai yiwuwa domin kawo Mana karshen ta’addanci a yankunanmu, saboda mutanen mu muna tsoron tafiye- tafiye ko zuwa gonakinsu,” ya fada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *