Peter Obi Ya Ziyarci Jonathan Gabanin Fara Yaƙin Neman Zaɓe

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, gabanin zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce shi da Jonathan sun yi musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi kasa a yayin ganawar.

Da yake raba hotunan ziyarar a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP ya ci gaba da cewa tattaunawar tasu ta shafi batutuwan da suka shafi muradun kasa gabanin zaben 2023.

“Kwanan nan na ziyarci babban yayana, H.E. @GEJonathan don yin musayar ra’ayi kan tarin tambayoyi masu muhimmanci na kasa. -PO,” Obi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *