Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) a jiya ta sha alwashin gurfanar da Gwamnatin Tarayya gaban ƙuliya kan rajistar Majalisar Dattawan Jami’o’in Najeriya (CONUA) da Kungiyar Malaman Likitoci ta Kasa (NAMDA).
Femi Falana, lauya ga ASUU, ya bayyana hakan a ranar Alhamis lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels Television na Sunrise Daily.
Ya bayyana rajistar kungiyoyin biyu a matsayin wanda ya sabawa doka.
“ASUU zata je Kotu. Wannan zai kasance hukuncin da zata ɗauka,” in ji Falana.
A ranar Talata ne Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya mikawa CONUA da NAMDA takardar shaidar rijista.
Ya ce Ƙungiyoyin biyu za su kasance tare da ASUU.
