Wani matashi a jihar Adamawa, Israel Emmanuel, yanzu haka ya shiga hannun jami’an tsaro na ‘yan sanda bisa shirin sace kan sa.
Bayan ya yi kokarin garkuwa da kan nasa ne, sai kuma ya nemi mahaifinsa ya biya kudin fansa Naira miliyan daya.
DAILY POST ta rawaito cewa a ranar Juma’a Isra’ila ya shiga cikin matsalar, bayan da ya kai karar wadanda suka hada baki wajen karbar kudin fansar.
Ya shigar da karar ke bayan da ya fahimci sun masa karya, ta hanyar karbar Naira miliyan 1, tare da cewa Naira Dubun dari biyar suka karba a wajen mahaifinsa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da cewa ta kama matashin Isra’ila da yayi wasan kwaikwayo da rundunar yan sandan da kuma mahaifinsa.
Sauran mutanen biyun da suka hada da Fartaci Kucol da Zakka Nuh daga karamar hukumar Mubi ta Arewa a arewacin Adamawa, wadanda su ma aka kamo su, sun amsa laifinsu.
Sun ce an ajiye Isreal na tsawon kwanaki shida a wani kauye mai nisa da ke Muvur a cikin karamar hukumar Mubi ta Arewa.
Yanzu haka rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike zata gurfanar da su gaban kotu.
