Rundunar Yansandan jahar Katsina a ranar Talatar nan ta tabbatar da mutuwar wani jajirtaccen jami’inta mai kula da tsaron shiyyar ta Dutsinma.
Ta tabbatar da hakan ne a cikin wani sakon manema labarai da mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isah ya aika ta manhajar WhatsApp.
Jami’in mai mukamin mataimakin kwamishinan Yansanda mai suna ACP Aminu Umar, ya hadu da ajalinsa ne a a garin Zakka da ke karamar hukumar Safana a yayin da shi da sauran jami’ansa da yan bangar da ke yankin su ke kokari dakile wani hari da yan ta’addan a saman bubura kimanin 300 da bindigogi tare da muggan makamai suka tunkaro cikin gari da nufin su shigo su kashe jama’a.
Mutane da dama na yaba kwazon jarumin jami’in Dan sandan bisa ga yadda ya ke jajurcewa wajen kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.
