Sama Da Magoya Bayan APC 13,000 Sun Koma PDP A Kaduna

Sama da mambobin jam’iyyar APC 13,000 ne suka fice daga jam’iyyar suka koma jam’iyyar PDP, a Kudancin Kaduna.

Ma’ajin jam’iyyar adawa ta Arewa maso Yamma, Hon. Rabiu Bakori, wanda ya karbi sabbin mambobin a madadin shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma, Sen. Hayatu Gwarzo, a yankin Zonkwa, ya ce idan har jam’iyyar ta ci zabe a 2023 dole ne kowa ya tashi.

“A shekarar 2015 jam’iyya mai mulki ta yi alkawarin inganta tsaro, amma ta kara sanya fargaba a zukatan ‘yan Najeriya.”

“‘Yan Kaduna su yi aiki tukuru don ganin PDP ta yi nasara a zabe domin tabbatar da adalci da gaskiya da kuma kimar dimokaradiyya ta gaskiya,” inji shi.

A nasa bangaren, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Hon. Felix Hassan Hyat, ya bayyana sauya shekar a matsayin alama kuma tarihi, ya kara da cewa za ta kai PDP gidan Sir Kashim Ibrahim, a 2023.

Ya kuma bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma daya tilo da PDP ke da karfi a Kudancin Kaduna, A cewarsa, “babu wata jam’iyya, sai dai PDP da ta taba cin zabe a Kudancin Kaduna, kuma zuwa 2023 babu wata jam’iyya da za ta ci zabe,” Hyat ya sha alwashin.

Sannan ya koka da yadda Kudancin Kaduna a karkashin jam’iyya mai mulki, ya fuskanci nakasu na ababen more rayuwa da kuma rashin tsaro mai yawa, inda ya ce yankin yana jin dadin nade-nade da samar da ababen more rayuwa ne kawai a lokacin gwamnatin PDP.

Haka kuma, Shugaban Matasan Jam’iyyar PDP na Kasa, Hon. Mohammed Kadede, ya ce sabbin mambobin sun fahimci cewa PDP ce jam’iyyar da ‘yan Najeriya ke bukata ta zo a 2023, domin kubutar da su daga mulkin APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *