Sanatoci hudu sun fice daga jam’iyyar PDP inda suka koma jam’iyyar APC, mai mulki.
A yayin zaman majalisar dattawa, shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya karanta wasikun sanarwar sauya sheƙa daga sanatocin. Sanata Aminu Iya Abbas na mazabar Adamawa ta Tsakiya, Sanata Amos Yohanna na Adamawa ta Arewa, da Sanata Ikra Aliyu Bilbis na Zamfara ta Arewa sun bayyana a hukumance cewa sun koma APC.
Kafin wannan, a ranar Talata, 10 ga Maris, Sanata Ipalibo Harry Banigo na mazabar Rivers ta Yamma ma ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, wanda ya zama sanata na hudu da ya koma jam’iyyar.
