Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi iya kokarin sa ga Najeriya.
Ya fadi haka ne a birnin Washington yayin da yake maraba da babban sakataren Abu Dhabi, Sheikh Al-Mahfoudh Bin Bayyah da mataimakinsa Fasto Bob Roberts na Amurka da suka kawo masa ziyara.
“Muna da girma a matsayi da yawan jama’a, muna fuskantar kalubale da yawa, amma a wurare da yawa, muna ƙoƙari. A cikin shekaru bakwai da rabi, na yi iya kokarina,” inji shi.
Buhari, a cewar sanarwar da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, ya ce magance matsalolin da suka addabi matasa shi ne abin da gwamnati ta sa a gaba, kasancewar su ne alkawarin da ta dauka na samar musu da makoma mai kyau.
Buhari, wanda ya yi magana game da bukatar tara matasa da ba su da tsattsauran ra’ayi.
Ya bukaci tawaga da ta ci gaba da yin tsari kan matasa wadanda su ne alkawurran nan gaba
