Shugaba Buhari Ya Yi Tsokaci Kan Kisan Lauya Ranar Kirsimeti, Ya Bada Tabbacin Ɗaukar Mataki

Shugaba Buhari Ya Yi Tsokaci Kan Kisan Lauya Ranar Kirsimeti, Ya Bada Tabbacin Ɗaukar Mataki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren ranar Litinin ya yi Allah wadai da kisan da wani dan sandan da ke bakin aiki ya yi wa Omobolanle Raheem, mamba a kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), a ranar Kirsimeti.

Daily Post ta ruwiato cewa, Buhari ya ce ya yi matukar kaduwa da bakin ciki da ya samu labarin kisan gillar da aka yi wa Raheem.

Shugaban ya kuma umurci hukumomin ‘yan sanda da su dauki “mafi kyawun mataki” kan wadanda aka kama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *