Sojoji Sun Farmaki Maboyar Yan bindiga, Sun Kubutar Da Mutum 3

Sojoji Sun Farmaki Maboyan Yan bindiga, Sun Kubutar Da Mutum 3

Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun ceto wasu mutane uku da akayi garkuwa da su a wani samame da suka kai maboyar ‘yan bindiga da ke kusa da babban yankin Kuriga-Manini-Udawa, da ke kan iyakar Chikun-Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da kula harkokin cikin gida Samuel Aruwan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ya ce sojojin da ke aiki da sahihan bayanan sirri sun gudanar da aikin bincike da ceto mutanen a maboyar da ke kusa da Ungwan Malam Ali.

“Da kai farmaki sansanin, sojojin sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su, Luka Ibrahim, Yusuf Jibril da Saminu Abdullahi.

“Sojojin sun kwato bindiga kirar AK47 daya, alburusai 18, da kuma harsashi guda 11,” in ji shi.

Aruwan ya ce an mayar da wadanda abin ya shafa ga al’ummarsu yayin da sojoji za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankunan baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *