Sojoji Sun Kashe Mutumen Da Ya Haddasa Harin Makarantar NDA

Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce sojoji sun kashe ‘yan ta’adda da dama a kewayen babbar unguwar tollgate a karamar hukumar Chikun ta jihar.

Kwamishinan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce daga cikin ‘yan bindigar da sojojin suka kashe, akwai Musti, wanda ya jagoranci wani mummunan hari a shekarar da ta gabata a Kwalejin horas da sojoji ta Najeriya dake Kaduna.

Ya ce Musti ne ya jagoranci harin wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an soji biyu na cibiyar, Laftanar Kwamanda Wulah da Laftanar Okoronkwo, yayin da wani Manjo Christopher Datong ya bace bayan harin da sanyin safiyar ranar 24 ga watan Agustan shekarar 2021.

Kwamishinan yace wani dan bindiga da ya yi kaurin suna mai suna Boderi Isiya, ya tsallake rijiya da baya, inda ya kara da cewa an samu gawarwaki da makamai a wurin, yayin da wasu daga cikin ‘yan ta’addan suka mutu sakamakon harbin bindiga.

Aruwan, ya kasa fitar da alkaluman ‘yan ta’addan da sojojin suka kashe.

Kwamishinan ya ce, “Shahararren dan fashin nan Boderi Isiya ya tsallake rijiya da baya, yayin da sojojin Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *