Tinubu ya taya Musulmi murnar bikin Sallah, ya bukaci hadin kai da kishin kasa

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmi murnar karamar Sallah (Eid-el-Fitr) bayan kammala azumin watan Ramadan.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar a Abuja, shugaban ya bukaci Musulmi da su sabunta kudurinsu na hadin kai, zaman lafiya da kuma hidima ga al’umma.

Tinubu ya ce ya kamata a ci gaba da amfani da darussan Ramadan kamar hakuri, sadaukarwa, tausayi da ibada ga Allah da jin kai ga jama’a, har bayan watan azumi.

Haka kuma, ya jaddada muhimmancin hadin kan ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, yana mai cewa hakan ne ginshikin zaman lafiya da ci gaban kasa.

Shugaban ya kuma bukaci Musulmi su rika taimakawa marasa galihu, domin karfafa zumunci da hadin kai a cikin al’umma.

Ya roki shugabannin addinai da su yi addu’o’in zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunkasar tattalin arziki a kasar.

Tinubu ya bayyana fatan cewa da hadin kan ‘yan kasa, Najeriya za ta shawo kan kalubalen da take fuskanta tare da samun ci gaba mai dorewa.

A karshe, ya yi wa Musulmi fatan murna da addu’ar samun albarka, fata da shiriya ga kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *