Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri Da Shugabannin Ƙungiyar Kiristocin Najeriya

Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri Da Shugabannin Ƙungiyar Kiristocin Najeriya

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya isa babban dakin taro na Christian Ecumenical Centre da ke Abuja domin ganawa da shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, kan zaben 2023 mai zuwa.

Tinubu ya isa tare da matarsa, Sanata Oluremi Tinubu; Kakakin majalisar Femi Gbajabiamila; Gwamnan Imo Hope Uzodinma; Gwamnan Ebonyi Dave Umahi da Sanata Smart Adeyemi da dai sauransu.

A baya dai ana ganin tsamin danganta ta yi kamari tsakanin Dan takarar jam’iyar ta APC da Kungiyar ta CAN tun bayan da ya bayyana Kashim Shatima a matsayin wanda zai masa mataimaki a zaben 2023.

Shatima dan Asalin jihar Borno ne dake yankin Arewa Maso Gasa, wanda kuma Musulmi ne kamar Tinubu. lamarin da CAN a baya ta yi Allah wadai da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *