Daga Amira Salisu Batsari
Tsadar Kayan Abinci Ta Ƙara Ƙamari A Yankin Kudu Maso Gabashin Nijeriya Bayan Ƴan Arewa Sun Ƙaurace Wa Yanki Kan Hare-haren IPOB
Shuwagabannin yan Arewa da suke gudanar da kasuwancinsu a tsakanin yankunan kudu maso gabashin Nijeriya da kuma Arrwa sun bayar da izinin ga yan arewa dake hada hadar kasuwancin kayan tireda da kuma direbobin manyan motoci dasu koma yankunansu a sabilinda kisan da Yan kungiyar masu Rajin Balle kasa wato Biafra sukeyiwa mambobin nasu.
Shugaban kungiyar Arewa Dr Auwal Abdullahi Aliyu ya bayyanawa majiyar Jakadiya cewa sun bayyana cewa sun bayar da gargadi tafiya yaji aiki na kwanaki ukku duba da kisan Babu gaira babu dalili da yan yanki kudu maso gabas ke yiwa Yan Arewa inda ya kara da cewa akallah Yan Arewa sama da mutum dari aka kashe acikin makon daya gabata.
Ya kuma bayyana cewa yajin aikin ya Zama dole domin dakatar da matasa Arewa daga daukar doka hannunsu idan aka cigaba kashe kashen.
Aliyu ya bayyana cewa yajin aiki wanda ya fara daga jiya Alhamis ya fara cimma nasarori inda ya kara da cewa ansanar da hukumomin tsaro da dukkanin gwamnonin Arewa da kuma yankunan da abun ya shafa.
Tun bayan da aka dakatar da hada- hadar manyan motoci masu Kai kayan abinci a yankin faranshi kayan abinci …a manyan garuruwan dake yankunan kudu masu gabas da kuma kudu maso kudu.
” Mun kulle hanyar data hada yankin Arewa da Gabas wanda suka hada da jihar Benue da Nasarawa da Kwara da Plateau da sauransu kuma direbobin sun bamu hadin kai,” ya bayyana.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar jihohin arewa guda Sha bakwai dake yankin kudancin Najeriya Malam Badamasi Muhammad ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa mafi yawan yan arewa dake zaune a kauyukan yankin kudu maso gabas sun koma gida dangane da tsoro da firgici akan hare haren da ake Kai masu, ya kuma bayyana cewa kadan ne daga cikin wadanda suke zaune a biranen yankin suka tsaya amma suma suna rayuwa cikin tsoro.
Ya bayyana cewa wadanda har yanzu suke zaune acen suma suna zaune don babu yanda zasuyi.
