Wani Hatsari Ya Hallaka Mutum 1, Ya Jikkata Mutane 3 A Ondo

Wani Hatsari Ya Hallaka Mutum 1, Ya Jikkata Mutane 3 A Ondo

Daga Amira salisu.

Mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da mutum ukku suka samu munanan raunika, a sanadiyyar wani hatsari da ya faru a ranar lahadi a dai-dai mahadar Osoro dake Ore-Ore a kan Babbar hanyar Benin a karamar hukumar Odigbo ta Jahar Ondo.

Kamfanin Dillancin labarai ya bada rahoton cewa, hatsarin ya faru tsakanin wata mota kirar Toyota Land Cruiser mai lamba FKJ 535 HP lagos da wata babbar mota mai lamba KRD 422 XB Lagos.

Shugaban Hukumar Kare Haɗurra ta kasa na yankin Ore, Mr Siriku Alonge ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai.

Ya bayyana cewa, direban karamar motar ya gagara dakatar da motar saboda mugun gundun da yakeyi sa’ilinda ya ya faɗawa Motar dake Ajiye a gefen hanya.

Ya bayyana cewa, wata mace daya dake cikin karamar motar ta rasa ranta tare da mutum biyu, da sauran Mutane biyu suka samu munanan raunika gami da direban Babbar Motar.

Alonge ya kara da cewa, ankai gawar a Asibitin morgue Opeyemi dake Ore, a yayinda aka tafi da sauran waɗanda suka jikkata a Asibitin domin karɓar magani.

Shugaban Hukumar ya kuma buƙaci Direbobi dasu guji mugun gudu domin tseratar da rayuka da dukiyayoyi domin iyalansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *