Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Hukumar Gudanarwar Jami’ar jihar Benue dake Makurdi ta bada umarnin gaggawar bude makarantar.
Daily Post ta bada rahoton cewa, Jami’ar BSU da sauran Jami’o’in Gwamnati sun kulle a ranar 14 ga watan Fabrairu, biyo bayan shiga Yajin Aiki da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa ta bayar.
Duk kokarin da Gwamnatin Tarayya tayi na shawo kan Yajin Aikin Ƙungiyar Malaman Jami’o’in yaci tura, inda ƙungiyar ta jaddada cewa sai an cika mata dukkanin bukatun ta kafin ta janye yajin aikin watanni 8.
A cikin wata sanarwar da magatakardar jami’ar Benue Mrs Mfaga Modom ta fitar a ranar talata, ta umarci dukkanin malaman dasu koma bakin aiki nan take.
A cewar sanarwar ” a madadin umarnin da shugaban makaranta ya bada Ina sanar da dukkanin malamai da mambobin jami’ar da sauran mutane cewa za’a bude makaranta daga ranar Laraba 28 ga watan Satumban 2022.”
” Ana bukatar dukkanin ma’aikata dasu koma bakin aiki daga ranar Laraba 28 ga watan Satumban 2022.”
Sanarwar ta bayyana cewa za’a sanar da ranar da dukkanin Daliba zasu koma.
A lokacin da Daily Post ta tuntuɓi Shugaban Ƙungiyar ASUU na Jami’ar Dr Kwaehfan Tarmombo ya Tabbatar da umarnin.
Ya kuma bayyana cewa malaman zasu koma kamar yadda aka bayar da dokar amma basu fara koyarwa ba har sai uwar kungiyar ta ƙasa ta dakatar da yajin aikin.
Ya bayyana cewa” wannan shine abinda muka fada amma har yanzu muna akan yajin Aiki, anyi Kira damu koma ofisoshinmu amma bazamu koyar ba,”
