Yan bindiga sun sace mutum 6 ciki harda Mata 2 yayin sallar Taraweeh a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun sace mutum shida daga cikin masu ibada yayin da suke gudanar da sallar Taraweeh a cikin wani masallaci a unguwar Azara da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis lokacin da maharan suka kutsa cikin al’umma suna harbe-harbe a iska, kafin su tafi da mutane hudu maza da mata biyu, abin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici da tashin hankali.

Wani mazaunin Azara, Tanimu Ibrahim, ya ce maharan sun kuma kai farmaki wani gida yayin da suke tserewa daga yankin inda suka sake sace wasu mutum biyu, sai dai cikin ikon Allah sun samu tserewa yayin da ake kokarin kaisu cikin daji. Wani jagoran al’umma da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana sunayen wadanda aka sace da suka hada da Saifullahi Harisu, Yakubu Yunusa, Abba Minkailu, Yusha’u Sadiku, Maryam Abdullahi da Aisha Yakubu.

Majiyar ta kara da cewa jagoran ‘yan bindigar ya tuntubi iyalan wadanda aka sace da misalin karfe 11 na safiyar Juma’a, inda ya nemi kudin fansa naira miliyan 30 kafin ya kashe wayarsa. Wata majiya daga ‘yan sanda ta tabbatar da sacewar amma ta ce a tuntubi Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna domin karin bayani, yayin da kakakin rundunar, ASP Hassan Mansur, bai fitar da wata sanarwa ba zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *