Yan sandan Katsina Sun Kama Wani Bursuna Da Ya Gudo Daga Gidan Yarin Kuje

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta ta bayyana cewa ta yi nasarar kama wani matashi da ya gudo daga gidan yarin kuje a Abuja bayan da yan ta’adda suka fasa gidan yarin a kwanan nan.

Kakakin rundunar SP Gambo Isah ne ya sanar da haka a ranar Juma’ar nan ta hanyar tura sakon sanarwar ta manhajar WhatsApp.

SP Isah ya ce wanda aka kama mai suna Abdulkadir Musa mai shekaru 30 dan asalin karamar hukumar Bakori a jahar Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *