Yanzu Ƴan Bindiga Sun Fi Gwamnati Ƙarfi Da Iko A Zamfara – Inji Wani Jigo

Wani dan asalin jihar Zamfara kuma dan kasuwa Alhaji Mohammed Modi ya koka kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jama’a da nakasa ‘yan kasa a jihar ya zama abin kunya da daure kai.

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da DAILY POST a Gusau, babban birnin jihar, Modi ya bayyana cewa ba a san takamaimai abin da wadannan ‘yan fashin ke bukata ba, yana mai nuni da cewa duk kokarin da ake yi na ganin sun yi hankoro da mika makamansu ya ci tura.

“Gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da ‘yan bindigar domin su rungumi zaman lafiya amma sun ki amincewa da matakin sulhu da gwamnati ta dauka.”

“Yanzu, babu wanda ke da ‘yancin yawo a cikin jihar, ko da da rana tsaka saboda mutane na tsoron a kashe su ko kuma a sace su.”

A cewarsa, gwamnatin jihar ta dauki matakan tsaro daban-daban domin kame wadannan munanan ayyuka amma abin ya ci tura.”

Sannan ya koka da yadda jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu amma daga dukkan alamu ‘yan ta’addan sun fi jami’an tsaro tsari da karfi a jihar.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *