An kara farashin kudin man fetur a Najeriya zuwa sama da Naira 165 a wasu sassan kasar nan, kuma gwamnati ce ta bada umarnin daukar matakin kamar yadda masu hada-hadar man suka ce.
Kawo yanzu Hukumar da ke Kula da Albarkatun Mai na Ruwa da kan Tudu ta kasa NMDPRA ba ta ce uffam ba game da wannan matakin na kara farashin man.
Wasu bayanai sun nuna cewa, karin farashin ya fara aiki daga yau Talata, inda har aka sayar da lita guda akan Naira 179 daga 165 a yankin kudu maso yammaci da kudu maso kudanci da kuma kudu maso gabashin kasar.
A can arewa maso yammacin Najeriya kuwa, farashin ya kai Naira 184 , sannan ana sayar da lita guda akan Naira 189 a yankin arewa maso gabashin kasar, abin da ke nufin an kara Naira 24 rigis a lokaci guda
Za a ci gaba da sayar da man fetur din akan Naira 179 a yankin tsakiyar arewacin kasar, yayin da a birnin Lagos za a ci gaba da sayar da farashin akan Naira 169, sannan kuma a Abuja farashin zai kasance akan Naira 174
