Zan Yaƙi Cin Hanci Da Rashawa Gadan-Gadan Kamar Yadda Shugaba Buhari Ya Yi – Tinubu

Dan takarar shugaban kasa, na Jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya sha alwashin ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tinubu ya ce wannan kuduri nasa zai tabbata ne idan ya yi nasarar hawa matsayin shugaban kasa.

Tinubu ya yi alkawarin ci gaba da sauye-sauyen da Buhari ya yi na ma’aikatan gwamnati don rage cin hanci da rashawa.

Ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake bayyana daftarin manufofin yakin neman zabensa a Abuja.

Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da rage barna a ma’aikatun gwamnati idan ya gaji Buhari a 2023.

An caccaki Tinubu kan cin hanci da rashawa da kuma tara dukiyar da ba za a iya ganowa ba.

Sau tari dai tsohon gwamnan na Legas ya ki amsa tambayoyi kan mallakar wani kamfani mai zaman kansa Alpha Beta da ke karbar haraji a madadin jihar kan wani kaso.

Ana kyautata zaton yana da babban hannun jari a kamfanin, wanda ya dauki nauyin kula da harajin Legas a karkashinsa a matsayin gwamnan jihar Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *