Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya ce ba tattaunawar siyasa suka yi da ɗan takarar shugabancin ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ba.
Obasanjo ya gargadi magoya bayan Bola Tinubu kan yaɗa cewa ya marawa takarar Tinubun baya a ganawar sirri da suka yi a gidansa da ke Abeokuta a ranar Laraba.
Ya ce yaɗa irin wadannan labarai marasa tushe na lahani ga ‘yan siyasa irinsu Tinubu.
A wata sanarwa da maitaimaka ma sa na musamman, kehinde Akinyemi ya fitar, Obasanjo ya ce ganawarsa da Tinubu ta ƴan uwantaka ce ba siyasa ba.
Wannan na zuwa ne bayan kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a wani taro na APC a Lagos ya ce ganawar Obasanjo da Tinubu alamar nasara ce garesu a zaben 2023.
Tsohon shugaba Obasanjo dai ya sake jaddada cewa shi uba ne ga duk ‘yan Najeriya da matasa da ke cikin kasar.
