Yajin Aiki: Tuni Malamai Suka Koma Gona, Tunda Gwamnati Na Horar Damu Da Yunwa – Shugaban ASUU

Yajin Aiki: Tuni Malamai Suka Koma Gona, Tunda Gwamnati Na Horar Damu Da Yunwa – Shugaban ASUU

Kungiyar malaman jami’o’i ta bayyana cewa malaman jami’o’in sun zabi yin wasu ayyukan da ba na ilimi ba domin samun rayuwa sakamakon yajin aikin da su ke yi.

ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu saboda inganta walwala, farfado da jami’o’in gwamnati da cin gashin kansu na ilimi da dai sauran bukatu.

Da yake zantawa da jaridar Punch, Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce matakin da gwamnati ta dauka na kin biyan bukatun kungiyar yana cutar dasu da al’umma.

A ranar Asabar din da ta gabata ne kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) da kungiyar masu zaman kansu ta NASU suka dakatar da yajin aikin da suke yi bayan da gwamnatin tarayya ta yi alkawarin biyan naira biliyan 50 na kudaden alawus-alawus na ma’aikatan jami’o’in da suka hada da ASUU.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *