Ku Sabunta Samfuran Apple Ɗinku A Ƴanzu Don Gudun Kutse – Pantami Ga Masu Apple, iPads
Ministan tattalin arzikin dijital Isa Ali Pantami, ya shawarci ‘yan Najeriya da su sabunta na’urorinsu na Apple kamar su iPhone, iPads da Macbooks, domin gujewa fadawa masu satar bayanan sirri, da neman sarrafa na’urorinsu.
Mista Pantami a ranar Asabar ya wallafa wani shirin na CNN na tsawon mintuna biyu a shafinsa na Twitter inda aka shawarci masu amfani da Apple da su hanzarta sabunta na’urorinsu don yaudarar masu kutse da ke amfani da babbar matsalar tsaro a IOS da ta gabata, don samun damar wurinsu, bayanan banki, hotuna da sauran bayanan sirri.
“Sabunta samfurin ku na Apple yanzu saboda babban lahani/rauni: Ku je zuwa Saitunan ku, sannan Gabaɗaya, sannan ku danna Sabunta Software,” in ji Mista Pantami.
Masanin kutse mai suna David Kennedy ya tabbatar da cewa matsalar na iya baiwa masu kutse damar sauraron hirarrakin masu amfani da wayar, da samun damar sakonnin tes, imel da kuma kyamarori. Ya jaddada cewa za a sayar da bayanan da aka yi wa kutse a kan miliyoyin daloli a kan yanar gizo mai duhu.
Don gudun kada a shiga cikin bayanansu da kuma yin gwanjonsu, ministan sadarwa ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su sabunta kayayyakin Apple.
“Ka sabunta samfuran Apple ɗinka a yanzu pls,” Mista Pantami ya rubuta.
Wasu masu sharhi sun caccaki ministan saboda musayar bayanai da suka rigaya a cikin jama’a, yayin da ya ci gaba da yin amfani da tashoshi na dijital don magance rashin tsaro.
