Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin mika jami’o’in gwamnatin tarayya ga gwamnatocin jihohi idan aka zabe shi a shekarar 2023.
Da yake jawabi a wajen bude taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya a Legas, Atiku ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta da albarkatun da ba su da iyaka, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
“Daya daga cikin muhimman gyare-gyaren da nake da shi a cikin takardar manufofina shi ne karfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu dangane da ci gaban kasa – na waje da na gida. Yana da matukar muhimmanci saboda gwamnatin tarayya ba ta da karfin yin duk abubuwan da suke son yi.
“Hanya daya tilo ita ce mu tabbatar da cewa an samar da yanayi mai kyau da masu zuba jari na gida da na waje za su shiga cikin ci gaban kasarmu, ko ta bangaren ababen more rayuwa, ilimi da kiwon lafiya.”
