Ƴan bindiga Sun Sace Kwamishinan Yaɗa Labarai Na Jihar Nasarawa

Ƴan bindiga Sun Sace Kwamishinan Yaɗa Labarai Na Jihar Nasarawa

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace Alhaji Lawal Yakubu, kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na Jihar Nasarawa.

Majiya a unguwar Nasarawa Eggon ta tabbatar cewa ‘yan bindigar sun bi sawun Kwamishinan zuwa gidansa.

Ya ce ‘yan bindigar sun kai yafi da Kwamishinan zuwa inda ba a san ko’ina ba tsakanin karfe 8:45 zuwa 9 na daren Litinin.

A cewarsa, biyo bayan sace Kwamishinan, “mazauna yankin sun faɗa cikin ruɗani sakamakon harbe-harbe da masu garkuwar suka rika yi da su kusan ƙarfe goma.

“Sun tafi da kwamishinan akan babur.”

DSP Ramhan Nansel, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ya bayyana cewa har yanzu babu bayanai game da yadda aka yi garkuwa da kwamishinan, a yayinda yake cigaba da jiran cikakken bayani akan haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *