Kungiyar Malaman jami’o’i (ASUU) za ta gana da wakilan Gwamnatin Tarayya kan yajin aikin da ta dade tana yi a yau Talata.
Shugaban Ƙungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata yayin da yake magana a gidan Talabijin na Channels a Shirin Siyasar mu A Yau, ya ce taron zai tattauna akan ɗaya daga cikin batutuwa bakwai da ASUU ke nuna rashin amincewarsu.
“Wannan shine batun sake tattaunawa,” in ji Osodeke.
“Sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009.
“Ba wai kawai batun albashi ba ne. Yana da alaka da tsarin Jami’o’i, kuɗaɗe, tsari, bayar da ƴancin cin gashin kai da sauran batutuwa da yadda jami’o’i zasu riƙa samun kudin shiga.
“Gwamnati ta rage shi zuwa albashi kawai. Amma da a ce sun duba duk yarjejeniyar kuma sun aiwatar da ita, da ba za mu yi maganar samar da kudade ba.”
Osodeke ya kuma bayar da shawarar cewa idan taron na ranar Talata ya yi kyau, za a iya janye yajin aikin.
“Muna shirye mu sanya hannu,” in ji shi.
