Yadda Ƴan sanda Suka Kashe Ƴan Bindiga, Suka Ƙwato Shanu A Ƙaramar Hukumar Kurfi

Yadda Ƴan sanda Suka Kashe Ƴan Bindiga, Suka Ƙwato Shanu A Ƙaramar Hukumar Kurfi

Rahotanni sun ce an kashe ƴan ta’adda da dama yayin da wasu da dama suka samu raunuka bayan ƴan sanda sun daƙile wani hari da suka kai kauyukan Dadawa da Barkiya da ke karamar hukumar Kurfi a jihar Katsina.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan ta’addan dauke da muggan makamai, wadanda adadinsu bai wuce 80 ba, sun far wa al’ummomin biyu da ke kan babura da misalin karfe 01:30 na safiyar yau Litinin.

SP Gambo ya kuma bayyana a cikin sanarwar cewa, an ƙwato dabbobin gida guda 110 a ƙoƙarin daƙile harin da aka kai kauyukan biyu.

Sanarwar a wani bangare na cewa: “Rundunar ta samu kiran gaggawa cewa ƴan ta’adda wadanda yawansu ya kai tamanin a kan babura, dauke da manyan muggan makamai, sun kai hari a kauyukan biyu, a lokaci guda, rundunar ta tura dakarunta zuwa yankin, tare da kama ‘yan ta’addan cikin wani musayar wuta .

“Ana fargabar an kashe ’yan ta’adda da yawa ko kuma an raunata su a yayin musayar wutar. Har yanzu dai tawagar ‘yan sanda na ci gaba da sintiri a yankin da nufin kamo ‘yan ta’addan da suka jikkata da kuma komo gawarwakinsu.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Idrisu Dabban Dauda a lokacin da ya ke yabawa kokarin jami’an na dakile ‘yan ta’addan ya bukaci jama’a da su ci gaba da baiwa jami’an tsaro hadin kai a yakin da ake yi da ƴan ta’adda a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *