Ƴan Bindiga Sun Saci Basarake Da Jigon APC Da Wasu Mutane 2 A Ondo

Daga Wakiliyar Mu Amira Salisu Batsari.

Wasu Ƴan bindiga da ake zargi da masu garkuwa da mutane, sunyi Garkuwa da Basaraken Iku Onika dake karamar hukumar Akoko ta Arewa Maso Gabas ta jahar Ondo, da Jigon APC Mukaila Bello da sauran yan asalin garin mutum 3.

Majiyar Jaridar Jakadiya, ta bada rahoton cewa, Anyi Garkuwa da Mutanen a daren ranar Alhamis akan hanyar Ago Panu dake kan hanyar Owo-Ikare.

Wadanda akayi Garkuwar dasu sun haɗa da da, Basaraken Gargajiya Yeye Gbafinro, Tsohon Ɗan Takarar Majalissar Dokoki na Ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa Maso gabas, sai kuma Shugaban Jam’iyyar APC Adeniran Adeyemo, da Shugaban Al’umma Bashiru Adekile.

Lamarin ya haifarwa Al’ummar yankin tashin hankali.

An bayyana cewa, wadanda aka kama suna kan hanyarsu ta komawa gida daga Akure Babban birnin jahar zuwa Ikare-Akoko, a lokacin da aka sace su akan hanya.

Direban Motar dake ɗauke da Mutanen Ƴan bindiga sun sare shi da adda, kuma yana cigaba da karɓar Magani a Asibitin Owo.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, masu garkuwa da mutane basu tuntuɓi iyalan wanda lamarin ya faru dasu.

Haka zalika, Rundunar Ƴan Sandan Jahar har yanzu bata yi jawabi kan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *