Sojin Sama Sun Yi Luguden Wuta A Dazuzzukan Zamfara Da Katsina, Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 45
Rundunar sojin saman Najeriya da ke aiki a jihar Zamfara ta kashe wani shugaban ‘yan bindiga, wanda aka fi sani da Dogo Rabe da wasu ‘yan kungiyarsa sama da 45 a dazuzzukan Zamfara.
Jami’an rundunar sojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a sansanonin ‘yan bindigar da ke tsakanin al’umomin Zurmi da Birnin Magaji a jihar Zamfara da Jibia a jihar Katsina, kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana.
Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa, kwanaki kadan kafin kai harin bama-baman, an kai wani hari makamancin wannan a sansanin na wani jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji da ke unguwar Fakai a jihar, inda aka kashe ‘yan bindiga a kalla 22, yayin da Turji ya tsere da rayuwarsa.
A cewar wata majiya daga yankin, Abdulbaqi Aliyu, harin na baya-bayan nan ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindiga a kalla 40 a yankin Birnin Magaji na jihar.
“Rundunar sojin saman Najeriya ta kai farmaki a dajin Sabon Birini Dan Ali, a karamar hukumar Birini Magaji, wanda ya yi sanadin kashe ‘yan fashin sama da 40,” inji shi.
An kai harin ne a lokacin da aka ce gungun na lodin shanun da suka sata.
