Wata Sabuwa: An sanya Sanatan PDP A Cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu
Wani jigon jam’iyyar PDP kuma Sanata mai wakiltar mazabar Enugu ta Gabas, Mista Chimaroke Nnamani, an saka shi a matsayin mamba a jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Presidential Campaign Council, PCC, gabanin zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa.
Nnamani, wanda tsohon gwamnan jihar Enugu ne mai lamba 350 a majalisar yakin neman zaben mai wakilai 422. An lissafta shi a matsayin memba na daraktan kananan hukumomi.
