Bana Cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa Na Jam’iyyar Labour Party – Aisha Yesufu

Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.

Mai Fafutukar kan akan siyasa da zamantakewar al’umma Aisha Yesufu ta ƙaryata jita-jita cewa an naɗa ta cikin Ƙwamitin Neman Zaɓen Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar Labour Party.

Mrs Yesufu ta kasance cikakkiya kuma daɗaɗɗiyar mai goyon baya data kasance tana yin awanni 24 a Kafafen Sadarwa na Zamani tana gangamin yaƙin neman zaɓe ga Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi.

Gabanin Zaɓen Shugaban Ƙasa na Shekarar 2023 jam’iyyar Labour Party ta fitar da jerin sunayen Kwamitin Yakin Neman Zabe daya kunshi mambobi dubu daya da dari biyu da talatin da daya, a satin daya gabata.

Majiyar Jakadiya ta bada rahoton cewa an fitar da jerin sunayen bayan kwanaki goma sha-hudu da fara yankin neman babban zaben shekarar 2023 mai zuwa, da aka buɗe a hukumance.

Akwai Jita-jitar data yi yawo cewa Akwai Sunan Aisha daga cikin jerin mambobin da aka naɗa a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe.

Amma a sakon data fitar a shafinta na Twitter a ranar Lahadi tace ” yaushe ne nake cikin mambobi masu yiwa Labour Party yakin neman zabe? Ina ganin yadda wannan karya ke yawo ko Ina.

” Bana daga cikin ƴaƴan jam’iyyar Labour Party kuma bana daga cikin jerin sunayensu. Ina mai sanar maku cewa ni Yar kasa ce kuma bana rike da wani mukami a kowane. Bazan yarda da bani wani muƙami ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *