Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Katsina, Alhaji Shafi’u Abd-Duwab, ya ce ficewar tsohon sakataren gwamnatin jihar, Mista Mustapha Inuwa, daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP cin amana ce.
Abdu-Duwab, wanda kuma shi ne Sakataren walwala na jam’iyyar APC na jihar, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadin nan a Katsina.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya tuna cewa Inuwa, wanda ya sha kaye a yunkurinsa na neman tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC, ya bayyana ficewar sa ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake jawabi ga magoya bayansa.
Ya bayyana cewa shawarar da Inuwa ya yanke na ficewa daga APC, nuni ne da cewa bai yarda da Allah ba.
“Ina ganin addu’ar da ya yi a baya da kuma furucinsa na amincewa da shan kaye ba a cikin zuciyarsa ba ne. Yana cikin mutanen da Gwamna Bello Masari ya baiwa damar da ba a ba kowa ba.
“Ya kamata ya yi imani cewa, duk yadda zai yi ya zama gwamna, idan Allah bai yarda ba, babu wanda zai iya yin hakan.
“Don haka bai kamata ya ci amanar jam’iyya da Masari ba bayan duk wani tagomashin da suka yi masa da sauran su.
