Zamu Ɗauki Nauyin Maganin Waɗanda Aka Kaiwa Hari A Benue – Saƙon Ta’aziyyar Buhari

Zamu Ɗauki Nauyin Maganin Waɗanda Aka Kaiwa Hari A Benue – Saƙon Ta’aziyyar Buhari

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a jihar Benue wanda rikicin makiyaya da manoma ya haifar.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Gbeji da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benue a ranar Laraba inda suka kashe akalla mutane 23 ciki har da dan sanda guda.

Bayan kwanaki uku da faruwar harin, Buhari ya kira gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, inda ya jajantawa al’ummar jihar ta Arewa ta tsakiya kan kashe-kashen da aka yi.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar ranar Asabar, shugaban ya ce babu wanda ya isa ya kaiwa kowa hari saboda salon rayuwarsa. Ya ce dole ne a ajiye siyasa a gefe domin dinke barakar da ke tsakanin ‘yan kasa.

“Babu wanda ya isa ya afkawa kowa saboda salon rayuwarsu. Haka kuma kada wani ya dauki fansa akan zaluncin da aka yi musu. Ya kamata dukkansu biyu su fuskanci hukunci kan abin da suka aikata, kuma a yi adalci,” in ji Shugaban kasar.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari da daukacin gwamnatin sa sun yi tir da hare-haren baya-bayan nan a jihar Benue. Ba abin yarda ba ne a ce makiyaya da manoma su kashe rayuka.”

Lokacin da irin wadannan bala’o’i suka faru, shugaban ya ce dole ne ‘yan Najeriya su tuna da cewa dukkansu ‘yan kasar ne daidai da kowa.

Haka kuma shugaba Buhari ya yi gargadin cewa gwamnatinsa za ta dauki nauyin wadanda aka farmaka da ba su ji ba su gani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *