Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya caccaki takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a daidai lokacin da yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 ke kara zafi.
Tinubu ya ce ba kamar Atiku ba, ba zai zama shugaban kasa na wucin gadi da ke raba lokacinsa tsakanin zama a Dubai da Najeriya ba.
Ya yi wannan jawabi ne a wata tattaunawa da ya yi da ‘yan kungiyar Tijjaniyya a Kano a jiya, kuma yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Tunde Rahman ya fitar.
Tinubu yayi alkawarin mayar da hankali wajen tunkarar kalubalen Najeriya da kuma shawo kan kalubalen.
A cewar Tinubu: “Na yi alkawarin ba da kashi 100 cikin 100 na lokacina da kuzarina wajen yi wa Najeriya hidima.
