Gwamnatin tarayya ta ce an dakatar da aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano saboda barazanar tsaro bayan harin da aka kaiwa jirgin kasa a watan Maris din 2022.
Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje, Honarabul Umar Ibrahim El-Yakub, ya bayyana hakan a lokacin da yake duba hanyar Kaduna ta gabas.
A wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da Jama’a, Blessing Lere-Adams ta fitar ranar Juma’ar nan, El-Yakub ya ce sabanin rade-radin da ake yi na cewa an yi watsi da kwangilar, nan ba da jimawa ba za a ci gaba da aikin saboda ingantaccen tsaro a kan hanyar.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa direbobi sun yi tir da halin da ake ciki a bangaren farko na babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano da ta hada Abuja da jihar Kaduna.
“Ana yin aikin ceto bayan an gano cewa hanyar ta tabarbare sakamakon ruwan sama. Nan ba da jimawa ba za a ci gaba da aikin gaba daya a kan hanyar saboda yadda ake samun ci gaba a fannin tsaro a yankin,” in ji Ministan
Sai dai ya ce ‘yan kwangilar sun dade suna aiki a kashi na biyu da na uku na hanyar, inda ya kara da cewa aikin ya kai matakin da ake so kuma za a kammala gudanar da aikin a kan lokaci.
Ya ce, “Har yanzu muna da kwarin gwiwar cewa za a kammala sashe na biyu da na uku daga yanzu zuwa kwata na farko na shekara mai zuwa. Duk da haka, sashe na ɗaya zai fi tsayi fiye da haka saboda wasu dalilai.
“Aiki a kan sassa na uku suna tafiya lokaci guda kafin harin jirgin kasa kuma an samu sama da kashi 50 na aikin a sashi na 1 kafin dan kwangilar ya dakatar da aikin saboda matsalar tsaro.”
Da yake magana kan yadda ake gudanar da aiki a east bypass da ke Kaduna, Ministan ya koka da yadda aka yi watsi da kwangilar da gwamnatin da ta shude ta bayar a shekarar 2002 har sai da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara aiki.
Ya bayyana cewa hanyar wucewar tana da jimillar gadoji 10: gadojin kasa hudu, gadojin kogi biyar da gada daya akan layin dogo.
