Ƴan Sanda Sun Cika Hannu Da Matsafin Da Suke Nema Ruwa Jallo A Osun
Rundunar Ƴan Sandan Jahar Osun tace ta kama wani da take nema ruwa a jallo a jihar Osun, mai suna Rasheed Hammeed da aka fi sani da Oko-Ilu.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar Ƴan Sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya fitar a watan Maris, ya ce ana neman Rasidi ne bisa laifukan kisan kai dake da alaƙa da tsafi, kone-kone, da kuma Fashi da Makami.
Oko-Ilu, ya kasance yana ta’addanci a yankin Ede, kuma ya zama ajalin mutuwar Mutane da dama, wanda Jami’an Hukumar Yaƙi da ƴan ƙungiyar asiri na Rundunar Ƴan sandan jihar suka kama shi.
An damƙe shi ne da misalin ƙarfe 4 na safe a Maɓoyar da yake, wanda yake a Babban Birnin Jihar kuma a halin yanzu yana hannun ƴan sanda.
Jami’an tsaro na zawarcin Rasheed, mai sana’ar walda, bisa zarginsa da kashe mutane da dama a yankin Ede.
Rasidi Baale Oko’lu’ ana zargin sa da hallaka Hassan Adedeji, wanda ya kammala babban Diploma a fannin sha’anin Kudi a kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya ta Ede.
A dalilin haka Rundunar Ƴan sandan jihar Osun ta bayyana cewa, duk wanda ya boye shi za a dauke shi a matsayin mai laifi.
